Skip to main content

Mahukutan Saudiyya sun ce mata za su iya zuwa Umrah ba tare da muharrami ba




 Ma'aikatar kula da aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayyana cewa daga yanzu mata za su iya aikin Umrah ba tare da muharrami ba.

Shafin Haramain Sharifain ne ya wallafa wannan labari na Facebook ranar Alhamis da daddare.

Shafin ya ambato ma'aikatar tana cewa daga yanzu mata ba sai sun kasance cikin wata tawaga ta 'yan uwansu mata ba domin zuwa Umrah.

A baya mahukuntan kasar sun amincewa mata yin Umrah ba tare da muharrami ba amma bisa sharadin cewa dole ne su kasance cikin wata tawaga ta mata.

A yanzu mata masu shekaru 18 zuwa 65 za su iya yin Umrah ba tare da muharrami ba.

Wasu na ganin sauyin taimaka wajen rage yawan kudaden da iyali da dama suke kashewa kan muharrami. Saboda idan ba su da miji ko kuma mazajensu ba za su iya tafiya ba, dole ne su zo da daya daga cikin 'ya'yansu maza ko wani dan uwa a matsayin muharrami.

Matakin dai wani bangare ne na sauye-sauyen zamantakewa da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya kaddamar, wanda ke kokarin bude tattalin arzikin kasar mai dogaro da man fetur.

Tunda ya zama yarima mai jiran gado an baiwa mata damar tuka mota da fita kasashen waje ba tare da wani mai gadi ba.


Madogarar Labarai: BBC

Comment Policy: Silahkan tuliskan komentar Anda yang sesuai dengan topik postingan halaman ini. Komentar yang berisi tautan tidak akan ditampilkan sebelum disetujui.
Buka Komentar
Tutup Komentar